<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><aka>Cika Mu da Ruhunka Allah</aka>
<title>Mai Taimako LW393</title>
<lyrics>[V1]
 Lokacin da sa'a ta yi kusa
 Da Yesu zai koma gun Uba.
 Ya tara fa, Almajiransa
 Sai ya ce zai koma, gun Uba.

[C1]
   Cika mu da Ruhunka Allah
   Ruhun Rai, Ruhu Mai Tsarki.
   Cika mu da Ruhun Iko
   Ruhun ƙamna, da hikima.

[V2]
 Kada zuciyarku ta ɓace
 Ba zan barku ba fa marayu.
 Amma zai aiko, Mai Taimako
 Ya bishe ku, cikin gaskiya.

[V3]
 Ruhun da Allahnmu ya ba mu
 Ba Ruhu ne na tsoro ba fa.
 Amma Ruhun Iko da ƙamna
 Cike da kuma fa hikima.

[V4]
 Ƴan'uwa mu yafa ƴaƴan Ruhu
 Farin ciki, ƙamna, salama
 Nasiha, tawali'u, nagarta
 Jimrewa, aminci, kamewa.</lyrics>
<hymn_number>393</hymn_number>
</song>